Gwamnatin Nigeria ta dauki matakan dakile shigowar cutar Ebola, cikin ta a daidai lokacin da hukumar dake dakile yaduwar cutuka ta kasa NCDC, ta fafada binciken matafiya a filayen tashi da saukar jiragen sama da manufar gano mutanen dake dauke da cutar in zasu shigo Nigeria.
:::Kafa jam’iyyar hadaka ba zai kayar da jam’iyyar APC ba—Masari
Sai dai shugaban hukumar ta NCDC, Dr Idris Jide, ya ce kawo wannan lokaci ba’a samu wani mutum daya daya shigo Nigeria da cutar Ebola ba, wanda gwamnati tace akwai bukatar yan kasa su kiyaye yin tafiye-tafiye zuwa kasashen da cutar Ebola ta barke.
Idan za’a iya tunawa tuni hukumomin kasar Uganda suka sanar da barkewar cutar tun a karshen watan Junairu, a yankunan Mbale Mukono, da Wasiko, wanda ta kashe mutum daya da kuma zaton kama mutane 44.