Auren Zawarawan Kano zai lashe Naira biliyan 2.5 a Shekarar 2025

0
29

Gwamnatin Kano ta sanar da shirin ta na kashe Naira biliyan 2.5, wajen gudanar da auren Zawarawa a fadin kananun hukumomin jihar 44 a wannan shekara ta 2025.

Kwamishinan kasafin kudin jihar Musa Shanono, ne ya sanar da hakan lokacin da yake zantawa da manema labarai akan abubuwan da kasafin kudin shekarar 2025 ya kunsa, bayan majalisar dokoki ta amince da shi.

Ya kuma ce za’a kashe naira biliyan 1, wajen ciyar da al’umma a watan Azumin Ramadan mai kamawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here