Rundunar yan sandan jihar Kano ta bayyana cewa ko kadan bata taba yin batun hana gudanar da taron Maulidin Tijjaniyya daya gudana a jihar ba a ranar 25 ga watan Junairu da muke ciki.
Kakakin rundunar yan sandan jihar SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya sanar da hakan a yau lokacin da rundunar tayi holin wasu mutane data kama wanda tace suna aikata laifin ta’addanci.
Kiyawa yace mutanen da suka kama sun hadar da yan kasar Chadi, da Nigeria, da suke aiki da kungiyoyin tayar da hankalin al’umma.
Yayin holin rundunar yan sandan ta bayyana Bama-baman data kama a ranar 24 ga watan Junairu gabanin taron Maulidin Tijjaniyya daya gudanar a jihar ranar asabar data gabata, wanda haka ne yasa suka bayyana cewa akwai bukatar al’umma su kiyaye, saboda an samu labarin shigowar bata gari cikin jihar Kano.
Kiyawa yace a lokacin da suka bayyana wannan magana anyi musu mummunar fahimta akan cewa sun hana taron Maulidin Tijjaniyya na jihar Kano, yana mai cewa ko kadan basu fadi haka ba.
Kiyawa, ya nemi al’umma su zamo masu kiyayewa da kuma taimakawa jami’an tsaro a koda yaushe.
Kafin yanzu dai gwamnatin Kano ta bayyana cewa babu batun matsalar tsaro kamar yadda yan sandan suka sanar, wanda hakan baya rasa nasaba da ganin yan sanda da akayi a filin wasa na Sani Abacha, da aka shirya gudanar da taron Maulidin tun da farko, bisa hujjar cewa Gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf, bai san da wannan magana ba.