A kowacce rana adadin dabbobin da ake yankawa na samun koma baya a jihar Lagos, kamar yadda mahautan jihar suka ce a yanzu haka shanun da suke yankawa basa wuce guda 3000, zuwa 5000, a rana.
:::Anyi rikici tsakanin matasa masu kwasar fetur daga motar data fadi da jami’an kwana-kwana
Kungiyar mahautan jihar ce ta sanar da hakan ta bakin shugabanta Alhaji Bamidele, Kazim, lokacin da yake zantawa da kamfanin dillancin labarai na kasa NAN, a birnin Lagos a yau alhamis.
Kazim, yace matsalolin wadatar kayayyakin more rayuwa da ake ciki a Nigeria shine dalilin da yasa hakan ta faru, yana mai cewa sun fara samun koma bayan yawan dabbobin da suke yankawa tun lokacin da aka fara rikicin Boko Haram, a shekarar 2015, sannan yace karyewar darajar naira da hauhawar farashin kayan masarufi ma ya taka rawa sosai.
Bugu da kari Kazim, yace tsadar da dabbobi keyi ya ta’azzara koma bayan cigaban harkokin fawa, saboda suna siyan saniya daya akan kudin da yakai naira miliyan 1 da dubu dari 7, wanda a baya kudin su bai wuce naira dubu dari 4, zuwa 5 ba.