Mahaifi ya kashe ‘yar cikin sa saboda ta saka bidiyon bai dace ba a TikTok

0
96

Mahaifin wata matashiya dan kasar Pakistan, ya hallaka yarsa sakamakon ya same ta da laifin saka wani faifan bidiyon da yace bai dace ta saka a kafar sada zumutar ba.

Mahaifin yarinyar mai kimanin shekaru 50, ya kashe ta a yau Alhamis, kwanaki kadan bayan ya dawo da iyalan sa gida daga kasar Amurka.

:::Mahautan jihar Lagos sun shiga damuwa saboda tsadar Shanu

Majiyar yan sandan kasar da ta tabbatar da faruwar lamarin tace mutumin yana zaune a kudu maso yammacin Pakistan, a birnin Quetta.

Shugaban yan sandan yankin da lamarin ya faru Babar Baloch, ya sanar da cewa yanzu haka mahaifin da yayi kisan yana hannun yan sanda, kuma ya amsa laifin kisan yarinyar tasa da bindiga, sannan yace taki bin umarnin daya bata na saka kayan da suka dace a jikin ta da kuma saka bidiyon da bai dace ba a TikTok.

Hukumar kare hakkin bil adama ta Pakistan, tace an kashe yan mata akalla 1000, a kasar saboda manufar kare martabar ahalin su, musamman idan mace ta aikata wani abun da yayi kama da zubar da mutuncin danginta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here