Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i, ya mayarwa da fadar shugaban kasa martani dangane da cewa in da an bashi mukamin ministan babu lallai ya rika sukar yanayin tafiyar da al’amuran APC da Gwamnatin Bola Tinubu.
Tunda farko dai El-Rufa’i, ya kalubalanci gwamnatin APC, da cewa ba zata iya magance matsalolin da ke damun Nigeria ba, tare da cewa bai dauke ta a matsayin jam’iyyar siyasa ba, bisa hujjar cewa ba’a gudanar da taron majalisar koli ba cikin Shekaru biyu, sannan yayi zargin ko wani mutum daya ne ya mamaye jam’iyyar.
Akan haka ne mai taimakawa shugaban a fannin yada labarai da sadarwa Daniel Bwala, ya tambayi El-Rufa’i, cewa shin da yana cikin kunshin ministoci zai yi wannan magana. ?
A martanin da ya mayar wa Bwala a wani sako da ya wallafa a shafin sa na X a yau Alhamis, tsohon gwamnan na Kaduna ya ce ko a gwamnatin Tinubu ya ke, zai fadi ra’ayin sa kan abin da ke faruwa a jam’iyyar APC.
El-Rufa’i yace zai yi magana ta sirri da wadanda abin ya shafa, sannan ya fito fili ya bayyana idan ba a dauki matakin daya dace ba.
Cikin sakon nasa El-Rufai ya ce ya fadawa shugaban kasa Tinubu cewa baya bukatar matsayi a gwamnatinsa.