Wasu da ake kyautata yan bindiga ne sun kashe wata mata da suka sace a gidan ta dake unguwar Chikakore, a Kubwa dake karamar hukumar Bwari a birnin tarayya Abuja.
A ranar litinin data gabata ne wasu mahara suka shiga gidan mamaciyar inda suka sace ta da mijinta mai suna Adesiyan Micheal, sai yaron su da wani dan uwan mijin, yayin harin da suka kai musu har cikin gida da tsakar dare.
:::Wani jirgin sama ya yi hatsari a filin jirgin saman Abuja
Rahotanni sun bayyana cewa bayan sace wadancan mutane yan bindigar sun kuma shiga wani gidan gona inda suka sace wani magidanci tare da jikkata matar sa, sannan suka tafi da karin wasu mutane 5.
Daya daga cikin mutanen dake makwabtaka da matar da aka kashe ya bayyanawa Abuja Metro, cewa an samu gawar a unguwar Ijah-Gbagyi, dake karamar hukumar Tafa, a jihar Niger, da sanyin safiyar ranar Talata.
Majiyar ta kara da cewa babban jami’in ofishin yan sanda na Kubwa, ne ya jagoranci dauko gawar tare da ajiye ta a babban asibitin Kubwa.
Haka zalika anyi zaton cewa matar ta rasu a lokacin da maharan ke tafiya zuwa daji, da haka zai sanya dole su kyale ta a nan don cigaba da tafiya da sauran mutanen da suka sace.
Kawo yanzu dai rundunar yan sandan birnin tarayya Abuja bata ce komai ba kan hakan.