Jirgin saman kamfanin Max Air mai ƙirar Boeing 737 wanda ya dauko mutane daga jihar Lagos zuwa Jihar Kano ya gamu da cikas yayin da yake kokarin sauka a filin tashi da saukar jiragen saman kasa da kasa na Malam Aminu Kano, dake birnin Kano.
Rahotanni sun bayyana cewa tayar jirgin ta gaba ta kama da wuta lokacin da ya sauka sannan goshin jirgin ya tunkuyi ƙasa da misalin karfe 10:45 na daren Talata.
Mutanen da abun ya faru a gaban idon su sun ce saukar jirgin ke da wuya tayar sa ta gaba ta fashe, kuma ta kama da wuta, wanda daga haka ne jirgin ya rika yawo yana neman kifewa, har sai da ya caki kasa.
Tuni dai ma’aikatan filin jirgin su ka magance yiwuwar konewar jirgin, inda fasinjoji suka tsira da rayuwar su babu ko jin rauni.
Manajan Kamfanin Max Air na Kano, Malam Bello Ramadan ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce ba a samu asarar rai ba.