Gwamnatin tarayya ta dakatar da kamfanin jirgin sama na Max Air, tsawon watanni 3.
Hakan ya biyo bayan yadda jirgin kamfanin yayi hatsari lokacin da zai sauka a filin tashi da saukar jiragen saman kasa da kasa na Malam Aminu Kano.
Hukumar kula da sifurin jiragen sama na cikin gida NCAA, ce ta sanar da daukar matakin.
:::Jami’an tsaro sun karbe iko da sakatariyar jam’iyyar PDP ta kasa bayan barkewar rikici
Wwannan shine karo na uku da jirgin Max, ke samun tangarda cikin watanni 3, da suka gabata.
Jirgin na Max, kirar 734, ya gamu da fashewar taya tare da kamawa da wuta a filin tashi da saukar jiragen saman kasa da kasa na Malam Aminu Kano, da misalin karfe 10:45, na daren ranar talata, da hakan ya sanya jirgin tunkuyar kasa da goshin sa duk da cewa babu daya daga cikin fasinjojin jirgin daya samu rauni.
Jirgin dai ya taso daga jihar Lagos, zuwa Kano.
Zuwa yanzu dai hukumar dake bincike akan faruwar hadura ta fara gudanar da bincike don gano musabbabin hatsarin.