Shalkwatar tsaron ƙasa ta yi cikakken bayani akan batun da ake yadawa cewa sojoji sun kama kasurgumin dan ta’adda Bello Turji, daya addabi Zamfara da jihohin dake makwabtaka da ita, ta hanyar yin garkuwa da mutane da kisan kai.
A kwanakin baya ne aka rika samun yada bayanai a kafafen sada zumunta masu cewa sojojin sun kama Turji, bayan wani harin da suka kai masa.
Shugaban sashin yada labarai na shalkwatar tsaron Nigeria Manjo Janar Edward Buba, ne ya ce babu gaskiya a zancen kamen Turji, sai dai suna son kama shi ido rufe.
Buba, ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da manema labarai, inda ya nemi al’umma su yi watsi da maganganun da akeyi na kama Turji.