Gwamnatin Benue zata bude gidajen Bredi a kanunun hukumomin jihar 23

0
70

Shugaban kamfanin kula da zuba hannun jari da kamfanoni ta jihar Benue Dr. Rayond Asemakaha, yace kamfanin zai fadada ayyukan sa zuwa bude gidajen Bredi a fadin kananun hukumomin jihar 23.

Asemakaha, ya bayyana hakan ne a yau lokacin da yake ganawa da kamfanin labarai na kasa NAN, inda yace manufar yin hakan itace samar da ayyukan yi ga yan jihar da kuma samar musu bredi mai inganci.

:::Sojoji sun kama mayakin kungiyar Boko Haram a jihar Taraba

Yace aikin fadada kamfanin samar da Bredin zai faro daga kananunu hukumomin Gboko, Otukpo, da Katsina-Ala.

Shugaban kamfanin ya kuma ce zuwa yanzu gwamnatin jihar Benue, ta dauki mutane 300, don yin aikin samar da Bredi, a shalkwatar kamfanin bredin dake Makurdi, da yace wannan abu ne mai kyau da zai habbaka tattalin arzikin jihar.

Masu kamfanonin Bredi masu zaman kansu a jihar sun nuna farin cikin su akan yadda gwamnati ta shigo cikin harkar, tare da fatan cewa gwanatin zata inganta fannin kasuwancin bredin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here