Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, yace yana yin rayuwa a yanzu da kudaden hayar da yake karba na daya daga cikin gidajen sa na jihar Kaduna, inda Buhari ya jaddada cewa shi fa bai aikata cin hanci da rashawa ba a lokacin mulkin sa don ya samu arziki.
Buhari, yace mulkin Nigeria abu ne mai matukar wahala, wanda ya roki shugabannin wannan lokaci su zamo masu aikata gaskiya da rikon amana.
:::Falasdinawa sun fara komawa gida bayan yarjejeniyar tsagaita wuta da Isra’ila
Tsohon shugaban kasar ya bayyana hakan ne a jiya lokacin da yake yin jawabi a gidan gwamnatin jihar Katsina, gabanin gabatar da zaben kananun hukumomin jihar da za’a yi a ranar 15 ga wata mai kamawa.