Babbar kotun jihar Kano karkashin mai shari’ah Sunusi Ado Ma’aji, ta bayar da umarnin dakatar da spetan yan sandan kasa daga yunkurin kama shugaban hukummar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, Muhyi Magaji Rimingado.
:::Falasdinawa sun fara komawa gida bayan yarjejeniyar tsagaita wuta da Isra’ila
Cikin hukuncin da kotun ta yanke ta kuma hana yan sanda gayyatar Muhyi ko yi masa duk wani abun daya danganci cin zarafi.
Daily News 24, ta rawaito cewa kwamishinan shari’ah na jihar Kano, hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Kano, da Muhyi Magaji, ne suka shigar da karar.
Masu kare kansu sune Babban speton yan sanda kasa, da mataimakinsa na shiyya ta daya dake Kano, da kuma kwamishinan yan sandan jihar Kano.
Babbar kotun ta jihar Kano, ta yanke hukuncin a yau litinin.
Idan za’a iya tunawa a makon daya gabata ne babban speton yan sandan kasa ya turo da wasu jami’ai daga Abuja, inda suka kama Muhyi, tare da tafiya dashi zuwa ofishin shiyya ta daya dake sharada a Kano, don amsa wasu tambayoyi.
A lokacin an bayar da belin Muhyi, bisa hujjar cewa zai kai kansa ga rundunar yan sandan kasa a yau litinin, wanda hakan ya samo asali akan takaddamar kwache wasu kadarorin da ake zaton tsohon gwamnan Kano, Ganduje, ya karkatar a zamanin mulkin sa da.