Fitaccen dan jaridar nan Mamallakin jaridar Daily Nigerian, Ja’afar Ja’afar, ya bayyana cewa mataimakin shugaban majalisar dattawa Sanata Barau I. Jibrin, yana da hannu dumu-dumu, a fitintinun da ake kunnowa jihar Kano, fiye da yanda wasu mutanen ke zargin hannun tsohon gwamnan jihar kuma shugaban APC, na kasa Abdullhai Ganduje, musamman a abubuwan da suka danganci siyasa.
:::Tinubu ya bukaci a kawo karshen fashewar motocin tankar mai a Nigeria
Bayanin hakan yazo cikin wani shiri da da Ja’afar Ja’afar, ke gabatarwa tare da dan jarida Nasir Salis Zango, da kuma mai fashin baki kuma lauya Bulama Bukarti, tare da Lauya Abba Hikima.
Yace a mafi yawancin lokuta su Barau, suna shirya maganganun da bana gaskiya ba, sannan su fadawa shugaban kasa cewa yanzu ba’a goyon bayan gwamnatin jihar Kano, yayin da Ja’afar yace dole su Barau, ba zasu so a bar gwamnatin Kano ta gudanar da taron al’umma ba saboda za’a gano cewa babu gaskiya a kalaman da suke fadawa shugaban kasa Tinubu, cewa yanzu gwamnatin Kano, bata da goyon bayan mutane, wanda hakan zai iya sakawa shugaban kasar ya daina amincewa maganganun su akan gwamnatin ta Kano, in aka hangi tarin mutanen da gwamnatin zata iya tarawa.
Ja’afar yace ko Babban jami’in dan sanda za’a kawo Kano sai wanda su Barau suke so za’a kawo.
Ja’afar yayi rantsuwa da Allah, akan cewa duk abubuwan da ake kullawa Kano mara kyau akwai hannun su Barau, a ciki.
Ja’afar, ya kara da cewa ko da Barau, yana son yin takarar gwamna a Kano, bai kamata ya shige gaba wajen shirya mata sharri ba.