An sace mutane 22 a kauyukan da yan sanda uku ne dasu a Kaduna

0
96

Wasu sabbin hare-haren yan ta’adda yayi sanadiyyar yin garkuwa da mutane 22, a kauyukan Kusheka, Kugauta, da Kitanda, a karamar hukumar Kauru ta jihar Kaduna.

Wata Majiya ta bayyanawa manema labarai cewa maharan sun fara sace mutane 12, a kauyen Kitanda, mafi yawancin su mata da yara, sannan suka sace ragowar mutane 10, a harin da suka sake kaiwa Kugauta, a ranar juma’a da daddare.

Wani mazaunin yankin mai suna Johnson, yace ayyukan rashin tsaro sun tsananta a yankin nasu, yana mai cewa babu cikakkun jami’an tsaro a inda suke saboda yan sanda uku ne kadai a garin.

Johnson, ya kara da cewa kusan kullum sai yan ta’adda sun kai musu harin sace mutane ko kisa, saboda yan sanda uku sun yi karanci wajen basu kariya daga maharan.

Daga bangaren biyan kudin fansa yace sun biya fiye da Naira miliyan 60, ga masu yin garkuwar, kuma har yanzu akwai mutane da ba’a saki ba.

Duk koƙarin jin ta bakin Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kaduna, DSP Mansir Hassan, ya ci tura.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here