Ganduje ne yasa aka kama ni, saboda kwace kadarorin sa—Muhyi Magaji Rimin Gado

0
89

Shugaban hukumar karbar koke koke da hana cin hanci da rashawa ta jihar Kano Barista Muhyi Magaji Rimin Gado, ya yi zargin cewa shugaban jam’iyyar APC na kasa Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya hada kai da rundunar yan sandan kasa wajen kama shi da aka yi a ranar juma’a, daga yan sandan birnin tarayya Abuja.

Daily News 24 ta rawaito cewa, Muhyi Rimingado, ya bayyana hakan a lokacin da yayi wata zantawa da kafar yada labarai ta DCL, yana mai cewa kamen da aka turo yan sanda daga birnin tarayya Abuja, suka yi masa wata ƙullalliya ce ake yi saboda hukumar da yake jagoran ta kwace wasu kadarorin da yace tsohon gwamnan Kano Ganduje, yayi amfani da hukumar (KASCO) wajen karkatarwa.

Muhyi, yace a zamanin mulkin Ganduje, an turawa hukumar samar da kayyakin noma ta jihar Kano KASCO, kudi naira miliyan dubu 4, da aka karkatar zuwa wasu bukatun kai da kai, kuma an samu hujjar cewa an tura wani kaso daga cikin kudin zuwa asusun gidauniyar Ganduje.

Shugaban hukumar yaki da rashawar ta Kano, yace kamata yayi a kyale shari’a tayi aiki akan ka’ida, ba wai a bawa masu laifi goyon bayan da zasu fi karfin doka ba.

Ya kara da cewa a yanzu haka maganar kwace kadarorin da ake kyautata zaton na gwamnatin Kano ne da aka karkatar zamanin Ganduje, tana gaban kotu kuma za’a ci gaba da shari’a ranar 26, ga watan Fabrairu.

Rimingado, yace babu wanda ya isa ya hana su kwace kadarorin da aka sacewa gwamnatin Kano, in har za’a yi amfani da hujjojin da hukumar sa ta tanada, inda ya ce babu abinda zai hana shi cigaba da daukar matakin shari’a akan zargin sace kudaden jihar Kano, kuma bazai yi kasa a gwuiwa ba.

Daga batun kamen da yan sanda suka yi masa, zuwa ofishin su na shiyya ta daya dake Kano, Muhyi Rimingado, yace sun yi maganganu da jami’an tsaro, sannan ya karbi belin kansa bisa hujjar cewa zai je birnin tarayya Abuja, a ranar litinin don kare kansa akan zargin da rundunar yan sanda keyi masa na karya ka’idar aiki a binciken wawure dukiyar Kano.

Sannan yace ko kadan hakan bai bashi tsoro ba saboda shi masanin doka ne.

Naira biliyan 4, shine kudin da hukumar Muhyi, ke zargin Ganduje, yayi amfani da mukamin sa wajen karkatarwa yayin da yake a matsayin Gwamnan Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here