An kori jami’an EFCC 27 daga aiki bayan sace kadarorin da hukumar ta kwato a hannun barayi

0
143

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta shiga tsaka mai wuya sakamakon satar kayayyakin da jami’an ta keyi bayan an kwato su daga wajen masu wawure dukiyar gwamnati.

Binciken jaridar Punch, ya bayyana cewa, an kori wasu jami’an hukumar, sannan wasu suna fuskantar tuhuma, bisa zargin su da almundahana, satar kadarorin da EFCC, ta kwato, wanda suka kunshi tsabar kudade da gwala-gwalaiZuwa yanzu an kori jami’an EFCC 27 daga aiki, saboda samun hannun su a laifin cin amanar hukumar a shekarar 2024.

Ko a ranar 6, ga watan Junairu na shekarar da muke ciki, sai da mai magana da yawun hukumar ta EFCC Dele Oyewale, yace suna gudanar da bincike akan wani zargin jami’in su da aka ce yayi zambar Dala dubu dari 4.

Haka zalika a kwanaki 2, da suka wuce an kama wasu jami’an EFCC, 10, dake jihar Lagos, saboda sace kayayyakin da hukumar ta kwato.

Abubuwan da jami’an na Lagos, suka sace sun kunshi Dala dubu dari 4, da kuma sarkokin gwala-gwalai na mata da darajar Kudin su takai Naira biliyan 1.

Majiyar Punch, data nemi a sakaya sunan ta tace tsadar rayuwa ce tasa jami’an EFCC suke sace kadarorin da hukumar ta kwato, tare da cewa ya kamata a dauki matakin dakile hakan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here