Shugaban kasa Bola Tinubu, ya sake bawa tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano, Nasir Yusuf Gawuna, mukamin shugaban bankin bayar da lamunin gidaje na gwamnatin Tarayya.
:::Tinubu ya kara bawa Ganduje Mukamin shugaban Hukumar Kula da filayen jiragen sama ta Kasa
Mai magana da yawun shugaban kasar Bayo Onanuga, ne ya sanar da hakan a yau juma’a cikin wata sanarwar daya fitar da safiya.
Kafin yanzu Tinubu, ya nada Gawuna a matsayin shugaban hukumar gudanarwar jami’ar Bayero, ta Kano.