Gwamnatin tarayya ta haramta ayyukan kungiyar Lakurawa

0
35
Sojoji
Sojoji

Gwamnatin Nigeria tace daga yanzu kungiyar Lakurawa ta zama ta yan ta’adda, sannan an haramta duk wani nau’in ayyukan kungiyar.

:::Gwamnatin Nigeria ta kashe Naira biliyan 9 wajen gyaran layin lantarkin arewa daya lalace

Kungiyar Lakurawa ta yan ta’adda ta fito a Nigeria cikin shekarar data gabata, wanda ta samo asali daga jihohin Sokoto, Kebbi da Zamfara.

A ranar alhamis data gabata ne gwamnatin ta shigar da wata kara gaban kotun tarayya dake birnin Abuja, wanda ta zargin kungiyar da aikata garkuwa da mutane da yin sace sace tare da kisan al’umma babu wani dalili, har ma da kisan jami’an tsaro da masu aikin gwamnati.

Babban lauyan gwamnatin tarayya Lateef Fagbemi, ya zargi Lakurawa da tunzura yan Nigeria su yi bore ga gwamnati, yana mai cewa ayyukan su barazana ne ga tsaron kasar.

Wadannan dalilai ne suka sanya gwamnatin tarayya neman kotu ta ayyana kungiyar Lakurawa a matsayin ta yan ta’adda.

Tuni dai Mai shari’a James Omotosho, ya haramta ayyukan Æ™ungiyar sannan ya ayyana ta a matsayin ta Æ´an ta’adda.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here