Gwamnatin jihar Adamawa ta sanar da fara shirin daukar matakin shari’ah akan duk iyayen da suka ki bawa ‘ya’yan su damar yin karatu.
Kwamishinan ilimi da cigaban al’ummar jihar Dr. Umar Garba Pella, ne ya sanar da hakan bayan gabatar da wani taron masu ruwa da tsaki a fannin ilimi.
Yace hakan yayi daidai da manufofin gwamnan jihar Ahmadu Fintiri, na inganta harkokin ilimi a Adamawa.
:::Tinubu ya bawa Gawuna mukamin shugaban bankin lamunin lamunin Gidaje
Kwamishinan ya kara da cewa wannan mataki da za’a dauka shine zai taimaka wajen kawo karshen matsalar kananun yaran da basa zuwa makaranta.
- \