Babu abinda zai hana gudanar da Maulidin Tijjaniyya a jihar Kano—Kwamared Waiya

0
73

Gwamnatin Kano tace babu wani dalili da zai hana yin da taron Maulidin Tijjaniyya, na kasa da aka tsara gudanarwa a jihar ranar asabar 25 ga watan Junairu.

Daily News 24 ta rawaito cewa, Kwamishinan yada labarai da al’amuran cikin gida na jihar Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ne ya sanar da hakan a daren ranar juma’a, lokacin da ya gudanar da wani taron manema labarai a fadar masarautar Kano.

Kwamishinan, yace sun samu bayanin cewa wasu jami’an tsaro sun rufe wajen da aka tsara gudanar da taron wato rufaffen filin wasa na Sani Abacha, dake Kofar Mata, tare da korar mutane daga wajen.

Gwamnatin ta Kano, tace babu wani dalili da aka samu da zai hana gudanar da taron wanda ya shafi sha’anin tsaro.

Tare da cewa yunkurin hana taron ya kasance wani rashin adalci.

A cikin jawabin da kwamishinan yada labaran, ya nemi gwamnatin tarayya data bayar da umarnin janye jami’an tsaron da suka mamaye filin wasan don bayar da damar gudanar da taron Maulidin Tijjaniyya na kasa kamar yadda aka tsara.

Waiya yace wajen taron mallakin gwamnatin Kano ne bana tarayya bane.

Sai dai an samu wata sanarwa daga rundunar yan sandan Nigeria reshen jahar Kano, mai cewa sun samu bayanan sirri na cewa ana shirin kawo harin ta’addanci Kano, musamman a wajen taruwar al’umma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here