Yan sanda sun kama Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano Muhyi Rimingado

0
119

Yan sanda sun kama Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano Muhyi Magaji Rimingado, a yau juma’a.

Wata majiyar data nemi a sakaya sunan ta, daga hukumar ta shaidawa talbijin ta TVC, cewa an kama Muhyi Magaji Rimin Gado, da yammacin yau a harabar hukumar dake birnin Kano.

Kawo yanzu ba’a samu cikakken dalilin kamen na Muhyi ba, sakamakon cewa mai magana da yawun ofishin yan sandan na shiyya ta daya dake Kano Bashir Muhammad, yace yana kan hada bayanai akan wannan batu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here