Shugaban Amurka ya nemi Rasha ta kawo karshen yakin ta da Ukraine

0
38

Shugaban kasar Amurka Donald Trump, ya yi gargadi mai karfi ga kasar Rasha, inda ya nemi shugaban kasar Vladmir Putin, ya gaggauta kawo karshen yakin da kasar sa ke gwabzawa da Ukraine.

:::Magidanci ya mutu bayan faɗawa rijiya a jihar Kano 

Trump, ya bayyana gargadin nasa a wani sakon daya aike ta shafin sada zumunta na Truth, wanda ya bayyana kalubalantar yakin da aka jima ana yi, tare da gargadin cewa zai dauki matakin karya tattalin azriki ga Rasha, in har aka ki kawo karshen yakin.

Trump, ya sanar da cewa sakamakon yakin tattalin arzikin Rasha, ya yi rauni, duk da cewa ya bayyana alakar dake tsakanin sa da shugaban kasar Rasha, wanda yace ba zasu manta da taimakon da Rasha ta yiwa Amurkawa ba, a lokacin yakin duniya na II, da yayi sanadiyyar mutuwar mutane miliyan 60. Sannan Trump, yace yana da alaka mai kyau tsakanin sa da Putin.

Shugaban na Amurka yace in har Rasha, taki yarda a kawo karshen yakin ta da Ukraine, ta hanyar tattaunawar sulhu ba, to babu makawa zai kakabawa kasar haraji, da kuma takunkumin karya tattalin arziki mai tsauri ga Rasha da masu taimaka mata a yakin. Amma Trump, yace zai jingine duk wadannan abubuwa daya lissafo da zarar Putin ya zabi samar da maslaha.

Idan za’a iya tunawa a yayin da Trump, yake yakin neman zaben shugabancin Amurka, yayi alkawarin kawo karshen yakin Ukraine da Rasha, a cikin awanni 24, bayan rantsar dashi.

Daga bangaren fadar gwamnatin Rasha Kremlin, itama ta nuna sha’awar samun daidaito da gwamnatin Trump, musamman yadda aka jiyo mataimakin ministan harkokin wajen kasar na cewa kalaman Trump, sun bayar da wata dama ta yin yarjejeniya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here