An sake samun tashin mummunar gobara a binin Los Angels na Amurka, kwanakin kadan bayan lafawar gobarar dajin data shigo birnin tare da haddasa mutuwar mutane da dukiya mai yawa.
Sabuwar gobarar ta tilastawa hukumomin Amurka, kwashe mutane don tsare rayuwar su daga salwanta, zuwa wani mastuginin da wutar bata kai ba.
:::Gwamnatin Thailand ta amincewa Daruruwan mutane sun yi auren jinsi
An samu tashin gobarar a jiya laraba, wadda ta faro daga yankin Castiac, mai dauke da gidajen mutane da makarantu, tareda tsaunika.
Karfin iskar dake tafe da gobarar ya sanya daga laraba zuwa yanzu ta ci girman kasa Kadada dubu 10, duk da cewa bata kashe ko da mutum daya ba, ko kuma lalata wajen mu’amalar mutane.
Gwanatin Amurka, tayi hasashen cewa jami’an ta zasu yi mai yiwuwa wajen kashe wutar kafin ta kai ga halaka bil adama.
Babban jami’in hukumar kashe gobara ta Los Angels, Anthony Marrone, ya sanar da cewa sabuwar gobarar dajin ta sha ban-ban da wadda aka yi fama da ita kwanan nan, da tayi sanadiyyar rayuwar kusan mutane 30, da kone matsuguni fiye da dubu 10, sannan yace an kashe kaso 15, cikin 100, na gobarar.