Ministan kudi da tattalin arzikin Nigeria, Wale Edun, yace lokaci bayan lokaci za’a rika sabunta farashin kiran waya dana Data a kasar.
Wale, ya sanar da hakan a lokacin da yake zantawa da kafar talbijin ta Arise, a yau Alhamis, yayin da yake wakiltar Nigeria a taron tattalin arzikin duniya na 2025, dake gudanar a birnin Davos, na kasar Switzerland.
:::Kaso 50 na Malaman jihohin Arewa basu Cancanci koyarwa ba–Tsohon Gwamnan Niger
A ranar litinin data gabata ne hukumar sadarwa ta kasa NCC, ta amincewa kamfanonin sadarwa su kara farashin kira dana Data da kaso 50, cikin 100, matakin da ya samu kalubalanta daga yan Nigeria, har ma da kungiyar kwadago ta kasa NLC, da tayi barazanar daukar mataki in aka gaza janye karin kudin.
Sai dai Edun, ya kare karin kudin da cewa hakan ya faru sakamakon tashin farashin kayayyakin da ake fuskanta a Kasa baki daya, kuma yace haka ne kadai zai sanya kamfanonin sadarwa su iya cigaba da gudanar da ayyukan su, tare da cewa lokaci bayan lokaci za’a rika bibiyar farashin kiran wayar don samar da daidaito tsakanin kamfanonin sadarwa da abokan huldar su, da kuMa yin adalci ga kowanne bangare.