A yau alhamis ne daruruwan mutane daga kasar Thailand, maza da mata suka samu damar gudanar da auren jinsi a tsakanin su, bayan amincewar da gwamnati tayi musu.
An kaddamar da amincewa da dokar bayar da damar auren jinsin ta hanyar daurawa wasu maza jaruman Fim aure.
:::Matashi ya hallaka mahaifiyarsa ta hanyar shake ta
Jaruman Fim din da aka daurawa auren na jinsi sune Apiwat “Porsch” Apiwatsayree, mai shekaru 49, da Sappanyoo “Arm” Panatkool, mai shekaru 38.
An daura auren nasu a ofishin daura aure dake birnin Bangkok, inda a nan ne aka bawa gardawan shaidar zama ma’aurata.
Masu sha’awar wannan hali sun sun nuna farin cikin su tare da cewa sun kwashe shekaru masu yawa suna neman a amince musu yin auren jinsin.
Shima Fira ministan Thailand, Paetongtarn Shinawatra, ya bayyana farin cikin sa da wannan doka, inda ya bayyana murnar sa a shafin sada zumunta na X.
Suma wasu tsaffin mata yan shekaru 64, da 59, sun yi nasu auren a yankin Bangrak.