Magidanci ya mutu bayan faɗawa rijiya a jihar Kano 

0
40

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta sanar da dauko gawar wani magidanci daya rasu sakamakon faɗawa rijiya a karamar hukumar Gezawa.

:::An saki matar Ike Ekweremadu daga gidan yarin Burtaniya

Kakakin hukumar kashe gobarar Saminu Yusuf, ya sanar da cewa sun samu labarin faɗawa rijiyar daga wajen wani dan sanda mai suna ASP Kabiru Abdullahi Lawan.

An samu gawar mutumin mai kimanin shekara 45, a garin Badawa, kuma har yanzu ba’a samu labarin wanda ya san shi ba, ko kuma yan uwan sa.

Har ila yau, ba’a san yadda aka yi mutumin ya fada rijiya ba, sai hango shi akayi wanda aka samu ya rasu bayan jami’an kwana-kwana sun ciro shi.

Yanzu haka dai hukumar ta miƙa gawar mamacin ga ofishin ’yan sanda na Gezawa domin neman danginsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here