Kungiyar kwadago ta nemi ministan lantarki yayi murabus

0
28
NLC
NLC

Kungiyar kwadago ta nemi ministan lantarki yayi murabus daga mukamin sa saboda durkushewar babban turken lantarki na kasa babu kakkautawa.

Shugaban kungiyar NLC, na kasa Joe Ajearo, ne ya nemi hakan cikin sanarwar daya fitar a daren talata, inda ya nuna matukar damuwar su, dangane da tabarbarewar fannin lantarki, wanda yace ya dauki hanyar durkushewa baki daya.

:::Bashin da ake bin Nigeria ya haura Naira Triliyan 142

Ajaero ya ce, Idan da ma’aikatar wutar lantarki na karkashin kulawar kwararrun jami’ai, da an kawar da rugujewar wutar lantarkin maimakon furucin da Ministan ya yi cewa za a ci gaba da fuskantar lalacewar wutar lokaci bayan lokaci.

Ajearo, yace wannan abu ya nuna a fili cewa babu kwarewa a aikin lantarkin Nigeria, don haka ya kamata ministan ya sauka don bawa wadanda suka dace damar kawo karshen matsalar wutar.

NLC, ta kuma kalubalaci naira biliyan 8, da ma’aikatar wutar ta nema don wayar da kan yan Nigeria su biya kudin lantarki, wanda ministan ya nemi haka a kasafin kudin shekarar da muke ciki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here