Bashin da ake bin Nigeria ya haura Naira Triliyan 142

0
16

Rahotanni sun bayyana cewa a yanzu haka ana bin gwamnatin Nigeria bashin da ya kai naira triliyan 142.3, daga ranar 30 ga watan Satumba, na shekarar 2024, wanda aka samu karin bashin da kaso 5.97, idan aka kwatanta da watan Yuni, na shekarar ta 2024, da ake bin kasar bashin naira triliyan 134.3.

:::NDLEA ta kama matasa masu safarar miyagun kwayoyi a Jihar Kano

Bashin ya kunshi na cikin gida da wanda aka ciyo daga kasasehn waje, wanda hakan ya yi tasiti matuka ga karyewar darajar naira saboda bashin ketare, idan aka kwatanta naira da dalar Amurka.

Wasu alkaluman ofishin kula da basuka na kasa DMO, yace bashin ketare ya karu da kaso 0.29, daga dala biliyan 42.90, zuwa dala biliyan 43.03, a tsakanin watan Yuni da Satumba.

Sai dai idan aka kwatanta da naira bashin ya karu da kaso 9.22, daga naira triliyan 63.07, zuwa triliyan 68.89, cikin watanni 3.

Alkaluman DMO, sun ce karya darajar naira ne musabbabbin karuwar bashin fiye da kima, wanda a watan Yuni kowacce dala daya take a farashin naira 1,470.19, inda ta tashi zuwa farashin naira 1,601.03, a Satumba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here