Masu hulda da kamfanonin sadarwa zasu kai karar NCC saboda karin kudin kira da Data

0
47

Kungiyar masu hulda da kamfanonin sadarwa ta kasa NATCOMS ta ce za ta shigar da hukumar sadarwar Najeriya NCC kara a gaban kotu saboda ta amincewa kamfanonin sadarwa sun yi karin kudin kiran waya dana Data da kashi 50 cikin 100.

A ranar 20 ga watan Janairu, ne hukumar NCC ta amince da bukatar kamfanonin sadarwa (telcos) ta kara kudin kiran.

:::Gwamnatin tarayya ta bayar da kwangilar gina titin Abuja zuwa Kaduna ga Kamfanin da ya dena aiki

Hakan ya faru bayan kungiyar masu lasisin sadarwa ta (ALTON) da kuma kungiyar kamfanonin sadarwa ta (ATCON) sun nuna damuwa akan kalubalen da suke fuskanta saboda hauhawar farashin kayyaki, wanda hakan ne yasa suka nemi yin karin kudin kiran waya dana Data da kaso 50 cikin dari.

Shugaban kamfanin sadarwa na MTN a Nigeria, Karl Toriola, yace ana son kara musu harajin da suke biya da kaso dari bisa dari dan haka suke son kara kudin da suke cajar mutane.

Da yake nasa jawabin shugaban kungiyar masu hulda da kamfanonin sadarwa,  Ogunbanjo, ya ce kungiyar su ta fahimci matsalar da masana’antar sadarwa ke fuskanta kuma ta bayar da shawarar a kara kudin kira daga kashi 5 zuwa kashi 10 cikin 100, amma sai aka samu karin kaso 50.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here