Donald Trump ya haramta bawa wadanda aka haifa a Amurka shaidar zama ɗan ƙasa

0
45

Shugaban Amurka Donald Trump, ya saka hannu akan dokar data kawo karshen bayar da shaidar zama ɗan ƙasa ga duk wanda aka haifa a Amurka, sai dai wadanda iyayen su ke zaune a kasar bisa tanadin doka.

Dokar anyi mata lakabi da “Kare ma’ana da martabar shaidar zama ɗan ƙasar Amurka” kuma shugaban ya saka hannu akan ta cikin ranar farko da ya karbi shugabancin kasar.

Dokar ta kunshi tanadin hana hukumomin Amurka bayar da shaidar zama ɗan ƙasa ga duk wanda iyayen sa suke zaune a kasar babu ka’ida, ko kuma wadanda basu da shaidar zama ɗan ƙasa ta din-din-din.

Daga ranar 19 ga watan Fabrairu mai kamawa Amurka zata hana bayar da shaidar zama ɗan ƙasa ga kananun yaran da aka haifa a kasar, da kuma kin yi musu fasfo din tafiye-tafiye.

Wannan doka na daya daga cikin karya manufofin tsohuwar gwamnatin Amurka karkashin Joe Biden, da kuma kokarin inganta manufofin Trump, na yaki da bakin haure.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here