Jami’an rundunar tsaron al’umma ta NSCDC, reshen jihar Katsina, sun kama wani ma’aikacin kamfanin rarraba wutar lantarki na jihar Kano (KEDCO), bisa zargin sa da sace mitar wutar lantarki a unguwar Tudun Wada, dake karamar hukumar Daura ta jihar Katsina.
An kama ma’aikacin mai suna Aliyu Muhammad, dan shekara 38, dake aiki a ofishin kamfanin rarraba lantarkin dake Daura, yayin da dakarun rundunar NSCDC, ke yin rangadi karkashin CSC, Bashir Umar Fago.
:::Cutar Anthrax ta shigo Nigeria
Mai magana da yawun rundunar ta Civil Defence, reshen Katsina, SC Buhari Hamisu, yace an kama ma’aikacin lokacin da ake zaton ya sace mitar wuta daga gidan wani mutum mai suna Alhaji Lawal Gadi, a ranar 16, ga watan Junairu 2025.
An samu mitar a hannun sa sannan an cigaba da gudanar da bicike akan Aliyu Muhammad, don gurfanar da shi a gaban shari’ah.
Kwamandan rundunar Aminu Datti, ya yabawa jami’an sa kan kokarin kama masu aikata laifi, inda ya jaddada aniyar su ta cigaba da dakile masu aikata laifuka a Katsina.