Za’a kashe kusan naira biliyan 2 wajen gyara turakun lantarkin da aka lalata

0
42

Manyan turakun lantarkin Nigeria na cigaba da fuskantar barazana daga wasu mutanen dake lalata su babu kakkautawa, duk da cewa jami’an hukumar tsaron al’umma ta farin kaya Civil Defence, na kokarin kiyaye duk wani abu da ka’iya samun turakun.

Rahotanni sun bayyana cewa a cikin kwanaki 5, da suka gabata an lalata manyan turakun dake rarraba lantarki har guda 18, a wasu jihohin kasar nan.

Kamfanin rarraba lantarki na Nigeria TCN, yace an lalata turakun a jihohin Rivers, Abia, da Kano, a tsakanin ranakun 9-14 na watan Junairu.

Cikin wata sanarwa da TCN, ya fitar ranar lahadi yace sai an kashe Naira biliyan 1 da miliyan dari 9, kafin a kai ga gyara turakun da aka lalata da gangan.

A ranar juma’ar data gabata ne masu lalata turakun suka illata babbar hanyar lantarkin da ta kawo wuta fadar shugaba Nigeria da wasu sannan Abuja, da hakan ya jefa wasu yankunan Abuja da fadar shugaban cikin duhu.

Masu aikata wannan laifi na lalata turakun lantarkin tare da sace manyan wayoyin wuta masu tsada, na kawo cikas ga fannin samar da wutar.

Shugabar sashin hulda da jama’a ta kamfanin TCN, Ndidi Mbah, tace tabbas irin wannan abun takaici da ake aiwatarwa na yin barazana ga samun kayayyakin more rayuwa, da samar da wuta a Nigeria baki daya.

Ko a ranar 10, ga watan Junairu sai da shugaban sashin rarraba lantarki na Fatakwal, Emmanuel Okpa, yace jami’an su masu rangadi sun iske an lalata wata babbar hanyar lantarki mai karfin KV 181, dake kai wuta Owerri zuwa Ahoada.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here