Sojojin Nigeria sun kashe ɗan Bello Turji, da yan ta’adda

0
44
Sojoji
Sojoji

Shalkwatar tsaron ƙasa ta tabbatar da kisan wasu yan ta’addan da suka addabi al’umma cikin su har da ɗan da fitaccen dan ta’adda Bello Turji, ya haifa.

Sanarwar shalkwatar tsaron ƙasa da kakakin ta Edward Buba, ya fitar tace, dakarun Sojin Nigeria masu atisayen Fansan yamma, ne suka kashe yan ta’addan bayan kai hari maboyar su, a ranar juma’a.

An samu nasarar kisan mutanen a dazukan Shinkafi, Kagara, Fakai, Moriki, Maiwa da Cindo.

Sanarwar ta ƙara da cewa sojojin sun ceto wasu daga cikin mutanen da Bello Turji ya yi garkuwa da su, sannan shi kuma Turji, ya samu nasarar gujewa farmakin dakarun.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here