Obasanjo da Buhari sun gurfana a gaban kotun Faransa akan kwangilar wutar Mambila

0
53

Tsofaffin shugabannin Nigeria Olusegun Obasanjo da Muhammadu Buhari, sun gurfana a gaban kotun kasuwancin duniya da ke birnin Paris na kasar Faransa, don bayar da sheda dangane da shari’ar da ake yi ta sulhu tsakanin gwamnatin tarayya da kamfanin samar da lantarki na Sunrise akan dala biliyan 2.3, da kamfanin yake nema a wajen gwamnatin Nigeria bisa zargin ta da karya yarjejeniyar kwangilar samar da wutar lantarki a Mambila.

Jaridar Daily trust, ta tabbatar da cewa yanzu haka tsaffin shugabannin na Nigeria, suna can birnin Paris, akan wannan dambarwar

Sai dai mai magana da yawun shugaban kasa Bayo Onanuga, ya musanta cewa gwamnatin tarayya ce ta tilastawa tsaffin shugabannin zuwa gaban kotu don bayar da sheda, inda yace sun yi hakan bisa son ransu da kuma son kare martabar Nigeria.

Mai taimakawa tsohon shugaban Nigeria Obasanjo, a fannin kafafen yada labarai, Kehinde Akinyemi, ya tabbatar wa Daily trust, cewa mai gidan sa ya tafi birnin Paris, duk da cewa bai bayyana abin da ya kai Obasanjo, kasar ta Faransa ba, bisa hujjar cewa bashi da wata masaniya akan dalilin tafiyar.

Daga bangaren tsohon shugaban Nigeria Buhari, kuwa an gaza samun karin haske daga mai magana da yawun sa Garba Shehu, saboda an gaza samun sa a waya, da kuma sakon da aka tura masa.

Amman duk da haka wata majiya tace Buhari, ya tafi birnin Paris, sai dai ba’a ji abinda ya je aiwatarwa ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here