Hukumar jin dadin alhazai ta kasa NAHCON, ta sanar da cewa Maniyyata Hajjin bana (2025) daga kudancin Nigeria zasu biya Naira miliyan 8 da dubu dari 7, sai Maniyyata daga Borno, da Adamawa zasu biya Naira miliyan 8 da dubu dari uku, don zuwa sauke farali a kasar Saudiyya.
Shugaban hukumar, Farfesa Abdullahi Usman, ya sanar da hakan a Abuja, ranar Litinin, ta hannun mataimakiyar daraktan yada labarai ta hukumar Fatima Usara.
Sanarwar da Usara, ta fitar tace mutanen da suka fito daga sauran jihohin arewacin Nigeria zasu biya Naira miliyan 8 da dubu dari 4, a matsayin kuÉ—in sauke faralin.
NAHCON tace an sanar da wannan farashi ne bayan dogon nazari da tattaunawa da masu ruwa da tsaki cikin su har da fadar shugaba Tinubu, da hukumomin jin dadin alhazai na jihohi.
Miliyan 8 da dubu dari 3, da 30, shine kudin aikin Hajjin Maniyyata daga Borno da Adamawa, zasu biya sai yan kudu da zasu biya miliyan 8 da dubu dari 70, da 80, yayin da sauran jihohin arewacin Nigeria zasu kashe naira miliyan 8 da dubu dari 4, da 60.