Donald Trump ya isa fadar shugaban Amurka White House

0
52

Zababben shugaban kasar Amurka Donald Trump, da zai sha rantsuwar kama aiki ya isa fadar gwamnatin kasar dake Washington DC.

Tuni dai Shugaban kasar mai barin gado Joe Biden da uwar gidansa Jill Biden suka gaisa da zababben shugaban kasar Donald Trump da matar sa Melania Trump lokacin da suka isa fadar White House.

Biden, ya wallafa hoton daya dauka na karshe a fadar White House, a matsayin shugaban Amurka, tare da mai dakin sa Jill Biden.

Ana sa ran mashahuran masu arziƙin duniya zasu kasance a wajen rantsar da Trump, saboda alakar sa da kasuwancin duniya.

Donald Trump, ya jaddada cewa zai yaki bakin haure a kasar da kuma mayar da hankali a fannin makamashi da tattalin arziki.

Haka zalika ya sha alwashin ganin ya daidai al’amuran dake wakana na yake-yake a yankin gabas ta tsakiya.

Da misalin karfe shida agogon Najeriya wanda ya yi daidai da sha biyun rana agogon Amurka za a rantsar da Donald Trump a matsayin shugaban Amurka na 47.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here