Civil Defence sun kama mutane 6 barayin babura a jihar Kano

0
44

Rundunar tsaron al’umma ta kasa (NSCDC) ta kama wasu mutane 6 da suka kware wajen sacewa mutane babura masu kafa biyu a jihar Kano.

Rundunar Civil Defence, tace mutanen sun kasance masu farmakar al’umma tare da yi musu fashin babur a unguwannin Gurin Gawa, da Bechi, dake karamar hukumar Kumbotso, wanda a yanzu haka suke a hannun rundunar don fadada bincike kafin a gurfanar da su a gaban kotu.

Bayanin hakan na cikin wata sanarwa da NSCDC, ta fitar mai dauke da sanya hannun jami’in hulda da jama’a na rundunar, SC Ibrahim Idris Abdullahi.

Matasan dake sace-sacen baburan sun hadar da Najib Lawal mai shekaru 25, sai Bashir Bello, mai shekaru 34, da Lawan Yakubu, shekara 27, sai Kabiru Garba, shekara 29, da Mubarak Basiru, Shekara 21, sai Kuma Hussain Hassan mai shekaru 24.

Sai dai har yanzu ana kan gudanar da bincike don kamo wasu biyu, daga cikin barayin da suka gudu.

Sanarwar tace a ranar 14, ga watan Junairu Mubarak Basiru da Hassan Hussain, sun shiga gidan wani mutun Abdullahi Bala, dake Gurin Gawa inda suka ci zarafin sa, tare da kwace masa babur.

An samu nasarar kama barayin da taimakon yan Bijilanti, da hakan ya sanya aka kai ga gano wasu baburan da aka sace guda biyu a wajen su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here