Kwamishinan yada labarai da al’amuran cikin gida na jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya jaddada aniyar sa ta yin aiki tare da masu ruwa da tsaki, cikin su har da Media Trust, don samun nasarar ayyukan da suka shafi ma’aikatar sa.
Waiya, ya bayyana hakan a lokacin da shugaban kamfanin Media Trust, Ahmad Ibrahim Shekaru, ya kai masa ziyarar taya shi murnar samun mukamin kwamishinan yada labarai da al’amuran cikin gida na jihar Kano.
Bayanin hakan na cikin wata sanarwa da Daraktan sashin ayyuka na musamman na ma’aikatar yada labarai da al’amuran cikin gida na jihar Kano, ya fitar.
A yayin ziyarar, Kwamared Waiya ya bayyana dadaddiyar dangantakar da ke tsakanin sa da Kamfanin Media Trust, inda ya tuna irin rawar da ya taka wajen samar da Trust TV da kuma shawarwarin da ya bayar domin ganin an kaddamar da ita cikin nasara.
Ya kuma yabawa Kamfanin Media Trust saboda juriyar da suka nuna ta fuskar sauya akalar yada labarai daga tsohon yayi na takardu zuwa aikin jarida a zamanance.
Kwamishinan ya bukaci Media Trust, da su ci gaba da kyakkyawan aikin da aka san su akai tare da mayar da hankali don bayyana muhimman batutuwan da suka shafi al’umma masu bukatar kulawar gaggawa.
Kwamared Waiya ya kuma yi alkawarin ci gaba da karfafa hadin gwiwa da Kamfanin Media Trust, domin inganta yada labarai masu inganci musamman wajen inganta manufofi da shirye-shiryen gwamnatin Jihar Kano.
A nasa jawabin, shugaban kamfanin Media Trust, Ahmed Ibrahim Shekarau, ya bayyana nadin Kwamared Waiya a matsayin wanda ya cancanta.