Farashin litar man fetur yakai naira 1,050, 1,150, bayan da matatar man fetur ta Dangote, ta sanar da karin farashin litar man daga naira 899, zuwa naira 955.
Farashin man ya danganta da gurin da za’a siya fetur din da kuma Defo-Defo, masu siyarwa yan kasuwa Mai.
Manyan dillalan mai sun tabbatar da hakan, tare da cewa farashin zai cigaba da yin sama in har farashin danyen man bai dakata da tashi a kasuwannin duniya ba, kamar yadda shugaban kungiyar manyan ma’aikatan fetur da iskar Gas, Fetus Osifo, ya sanar.
A ranar alhamis farashin danyen man yakai dala 80, akan kowacce ganga daya, wanda a baya ake siyar da shi akan dala 73.
A ranar juma’ar data gabata ne matatar man fetur ta Dangote, ta kara farashin litar man, zuwa 955, wanda haka ya tabbatar da cewa dole ne farashin ya canja a gidajen mai.
Tuni dai jaridar Punch, ta rawaito cewa kawo wannan lokaci farashin man yakai naira 1,050 zuwa 1,150, a wasu gidajen mai, bayan sanarwar canjin farashin matatar Dangote.