Gwamnatin kasar Isra’ila ta kammala amincewa da yarjejeniyar tsagaita wuta a yakin ta da Hamas, wanda yayi sanadiyyar mutuwar dubban Falasdinawa, da kuma lalata musu kasa, wanda aka shafe fiye da shekara guda ana yi.
Tuni dai ministocin Isra’ila suka yarda da yarjejeniyar, da zata bayar da damar yin musayar fursunonin yaki tsakanin Isra’ila da Falasdinawa, da kuma dakatar da kai dukkanin wasu hare hare.
Majalisar ministocin ta amince da yarjejeniyar ce bayan shafe lokaci mai tsaho suna tafka muhawara akan yiwuwa ko janye yarjejeniyar.
A gobe lahadi ne ake kyautata zaton yarjejeniyar tsagaita wutar zata fara aiki.
Tsagaita wutar yakin zata bayar da damar sakin fursunonin Falasdinawa, wanda itama Hamas, zata saki yan Isra’ila uku da take rike dasu, sannan Isra’ila zata janye sojojin ta daga matsugunan Falasdinawa.
Wasu ministocin Isra’ila masu ra’ayin rikau ne suka so kawo wa tsagaita wutar tangarda, inda suka yi barazanar ajiye mukamin su da zarar an yarda da yarjejeniyar.