Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta kasa EFCC ta bankado wani waje da ake kyautata zaton cewa ana koyar da damfara a birnin Benin na jihar Edo.
EFCC ce ta sanar da hakan cikin wata sanarwa data fitar a shafin ta na X a ranar alhamis data gabata, sannan tace an kama mutane 25, masu damfarar mutane a wajen.
Sanarwar tace, EFCC ta samu nasarar kama mutanen a harin da takai bayan samun bayanan sirri akan cewa ana yin amfani da wani gini don koyawa matasa damfarar Yahoo, da saurin nau’in cutar mutane a kafar internet.
Cikin abubuwan da EFCC ta kama a gurin koyar da damfarar sun hadar da motoci guda 6, da na’ura mai kwakwalwa wato (Computer).