Wasu fusatattun matasa sun kona babur din Adaidaita Sahun, da ake kyautata zaton na masu satar waya ne akan titin Ibrahim Taiwo, a birnin Kano.
Bayan kone baburin an kuma yi nasarar kama masu babur din tare da mika su hannun jami’an tsaro.
Kakakin Rundunar ‘Yan sandan Jahar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da faruwar lamarin, sannan ya ce wadanda ake zargin suna hannun jami’an tsaro.
Kiyawa, yace an samu waya guda biyar a wajen su.
Lamarin dai ya faru a daren yau asabar.
Satar waya a wajen wasu daga cikin masu baburi mai kafa uku ta zama ruwan dare a wasu sannan jihar Kano, wanda irin haka ta faru kwanakin baya a kofar shiga asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano, da aka samu wasu masu sace waya a babur inda aka kone musu babur din suma.