Matatar Dangote ta kara farashin litar fetur zuwa 955

0
21

Matatar man fetur ta Dangote ta sanar da karin farashin man fetur akan kowacce litar daga naira 899, zuwa naira 955, ga dillalan man.

Jaridar Punch, ta rawaito cewa shugabannin matatar Dangote, sun sanar da hakan ne a yau juma’a.

Sanarwar tace duk wanda zai siya litar mai daga miliyan 2 zuwa miliyan 4.99, zai siya a farashin naira 955, sai wanda zasu siya lita miliyan 5, zuwa sama da za’a basu a farashin naira 950.

Sabon farashin zai fara aiki a yau juma’a da misalin karfe 5:30, na yammaci.

Karin farashin baya rasa nasaba da tashin farashin danyen mai a kasuwar duniya, daga dala 73, a kowacce ganga zuwa farashin daya haura dala 80.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here