Gwmanatin tarayya ta sanar da lokacin kammala aikin titin Abuja zuwa Kano

0
54

Ministan yada labarai, da wayar da kan al’umma Muhammad Idris, yace shugaban kasa Bola Tinubu, ya damu matuka wajen kammala aikin titin daya taso daga Kano zuwa Abuja, wanda hakan yasa gwamnatin ta kwace aikin wani bangaren titin daga hannun kamfanin Julius Berger, da ya faro aikin tun farko, zuwa wani kamfanin na daban don samun nasarar kammala aikin akan lokaci.

Ministan, ya bayyana haka a jiya alhamis lokacin daya kai ziyara wajen aikin titin a garin Tafa dake jihar Niger, don ganin yanda aikin ke gudana.

Muhammad Idris, ya kai ziyarar ce tare da ministan ayyuka Dave Umahi, da kuma shugaban kwamitin ayyuka na majalisar dattawa Mpigi Barinada, sai kuma shugaban kwamitin ayyuka na Majalisar wakilai Akinola Alabi, da sauran su.

Ministan yace tabbas Tinubu, ya matsu a kammala aikin titin, sannan yace ba za’a dagawa kamfanonin dake aikin kafa ba, zuwa wasu shekaru uku ba tare da kammala aikin titin ba.

Ministan ayyuka Dave Umahi, yace kamfanonin dake aikin sun ce nan da watanni 14, masu zuwa zasu gama aikin titin, yana mai cewa shi kansa ya ganewa idon sa kokarin da kamfanonin keyi Kuma zasu iya cika alkawarin da suka dauka, ya Kuma nemi a dena siyasantar da batun aikin na titin Abuja zuwa Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here