Gwamnatin Kano, ta kudiri aniyar samar da wata ma’aikatar musamman da zata tabbatar da wadatar lantarki a jihar, don bunkasar tattalin arziki.
Bayanin hakan ya fito ta bakin kwamishinan yada labarai, na jihar Ibrahim A. Wayya, lokacin da yake zantawa da manema labarai.
Wayya, yace Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, yana da manufar gyara wasu manufofin gwamnati da suka shafi bunkasar tattalin arziki da inganta cigaban jihar, musamman a fannin kasuwanci.
A. Wayya, yace a yanzu haka ma’aikatar yada labarai da al’amuran cikin gida ta Kano, ta cigaba da yin wasu ayyukan da a baya ma’aikatar bata yi saboda wasu dalilai.
Ya kuma ce bayan karbar shugabancin ma’aikatar yada labarai, ya gano cewa ba ma’aikatar ce ke gudanar da ayyukan da suka rataya a wuyan ta ba, sai wani mutum na daban.
Cmr. Waiya ya Æ™ara da cewa zuwa yanzu sun dawo da kaso 85, cikin dari na ayyukan da ma’aikatar yaÉ—a labarai da al’amuran cikin gida take yi mako É—aya da zaman sa sabon Kwamishinan yaÉ—a labarai.
Daga karshe Wayya, yace daga zuwan sa ya kirkiro sabbin cigaba a ma’aikatar yada labarai ta Kano.