Ya kamata sarkin Kano ya daina nuna son rai—Fadar shugaban kasa

0
61

Gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu, ta nemi sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II, ya daina nuna son rai da wariya tare da neman ya mayar da hankali wajen inganta cigaban al’ummar Nigeria.

Fadar shugaban kasar ta sanar da haka a matsayin mayar da martani ga kalaman sarkin na cewa ba zai bayar da shawara ga gwamnati ba akan yanda zata tsara wasu manufofin da zasu bata nasara.

:::Karnuka sun kashe wata yar Nigeria a kasar Italiya

A ranar Laraba ne dai Sarki Muhammadu Sanusi II a yayin taron tunawa da fitaccen lauyan Najeriya, Chief Gani Fawehinmi karo na 21 a Lagos, ya yi kalaman da suka harzuƙa gwamnatin.

Sarki Sanusi ya bayyana cewa yana da bayanai kan wasu abubuwa game da halin da Najeriya ke ciki da hasashen abin da zai iya faruwa da kuma yadda za a iya kaucewa hakan, sai dai ya ce ba zai bayyana hakan ba, domin idan ya yi hakan zai taimaki gwamnati, shi kuma ya ce ba zai taimaki gwamnatin Tinubu ba.

Cikin wata sanarwa da ministan yaÉ—a labarai Mohammed Idris ya fitar, yace a baya sarkin ya nuna amincewa da tsare-tsaren da gwamnatin ke dauke, sai kuma a yanzu da baya tare da shugaban kasar yake nuna cewa ba’a yin abun daya kamata.

Sanarwar ta kara da cewa bai kamata mutum kamar sarkin ya fito fili yana fadar abubuwan da ba gaskiya ba, saboda yana zaton ana nuna masa kiyayya.

Gwamnatin Tinubu tace ba ta buƙatar amincewar Sarki Sanusi kan muhimman manufofinta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here