Kungiyar kasashe masu arzikin man fetur ta duniya OPEC, ta sanar da cewa fara aikin da matatar man fetur ta Dangote, dake Nigeria, tayi ya yi tasiri ga yanayin tafiyar kasuwar man fetur a nahiyar Turai.
Matatar Dangote, dai ta fara aiki a cikin watan Junairun shekarar 2024, sannnan tana da karfin tace gangar mai dubu 650, a kowacce, rana.
:::Ya kamata sarkin Kano ya daina nuna son rai—Fadar shugaban kasa
A watan Satumba, na 2024, ne matatar ta fara fitar da man fetur, a Nigeria, wadda ta dogara kacokan akan shigo da fetur daga ketare.
Daga lokacin da matatar da fara aiki ta himmatu wajen fitar da man jirgi, man Dizel, da fetur, zuwa wasu kasashen nahiyar Afrika, da sauran su.
OPEC, tace daga lokacin da matatar Dangote, ta fara aiki an samu raguwar shigo da mai Nigeria daga Turai, kamar yadda kungiyar ta sanar a jiya laraba.
Idan za’a iya tunawa mujallar Bloomberg, tace matatar fetur ta Dangote, tafi matatun man fetur 10, manya dake nahiyar Turai, a fannin karfin tace fetur mai yawa.
Babbar matatar da tafi kowacce karfin tace man fetur a rana daya a nahiyar turai itace Pernis, mai tace ganga dubu 404.