Rundunar sojin kasar nan ta tattabar da kisan yan ta’adda 6, lokacin da sojoji suka kaiwa mayakan Lakurawa, hari a karamar hukuar Gudu ta jihar Sokoto.
Mai magana da yawun rundunar hadin gwuiwa ta atisayen Fansan Yamma, Laftanar Kanar Abubakar Abdullahi, ne bayyana hakan cikin wata sanarwar daya fitar yana ai cewa sojoji 5 sun mutu a yayin artabun da suka yi da yan ta’addan.
Yace dakarun sun samu nasarar gano makamai da suka kunshi bindiga da alburusai.
Abubakar, yace akwai bukatar al’umma su zama masu bin diddigin duk wasu abubuwan rashin tsaro da ka’iya afkuwa a yankunan su, da kuma kai rahoto ga mahukunta don daukar mataki akan lokaci.
Sanarwar tace samun hadin kan al’umma zai bawa jami’an tsaro damar kawar da ta’addanci cikin kankanin lokaci.