Karnuka sun kashe wata yar Nigeria a kasar Italiya

0
31

Wata ‘yar Najeriya mai shekaru 27 mai suna Patricia Masithela, ta rasa ranta bayan da wasu karnuka masu fama da yunwa suka yi mata fata-fata a garin Latina na kasar Italiya.

Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Litinin da daddare yayin da Patricia ke ziyartar wani saurayin ta a gidansa da aka yi watsi da shi tsawon lokaci a yankin Lazio, kamar yadda mujallar Mirror UK ta rawaito.

Ihun Patricia, ne ya ankarar da mutane abinda ke faruwa har akayi kokarin ceton ta, amma anyi rashin sa’a karnukan sun kashe ta.

Patricia, ta koma Lazio kwanan nan daga Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here